1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Tinubu ya nada sabon gwamnan CBN

September 15, 2023

Shugaban na Najeriya kuma ya sanar da nada mataimaka guda hudu ga sabon shugaban babban bankin na CBN. Mataimakan sune; Emem Nnana Usoro da Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Philip Ikeazor da Bala M. Bello

https://p.dw.com/p/4WOny
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da nada Dr. Olayemi Michael a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya Ajuri Ngelale ya aike wa DW Hausa, Shugaba Tinubu, ya ce Dr. Micahel zai jagoranci bankin na CBN na tsawon shekaru biyar, idan har Majalisar Dattijan Kasar ta tabbatar da nadin nashi.

Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Tinubu na sa ran wadannan manyan jami'ai za su taimaka wa kudurin gwamnatinsa na farfado da tattalin arzikin kasa tare da cire 'yan Najeriya daga cikin radadin rayuwa da suke ciki.

Wadannan nade-nade dai na zuwa ne makonni bayan dakatar da Godwin Emefiele daga kujerar gwamnan CBN bayan da sabuwar gwamnatin Najeriya ta zarge shi da aikata ba daidai ba. To sai dai wasu na ganin matakin a matsayin bita-da-kulli na siyasa da sabuwar gwamnatin ta yi wa Emefiele domin ladabtar da shi kan sauya fasalin takardar kudi ta naira da ya bijiro da ita a lokacin yakin neman zabe, da a lokacin aka yi zargin ya yi haka ne domin hana Shugaba Tinubu lashe zaben Najeriya.