1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Tsamin dangantaka da Ukarine

Ihor Burdyha WB/ATB/LMJ
August 6, 2024

Kasar Mali ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine, bayan da gwamnatin Bamako ta soki lamirin kalaman da hukumomin leken asirin sojan Kyiv din suka yi a game da wani hari da ya halaka sojojin Mali da sojojin hayar Rasha.

https://p.dw.com/p/4jBEk
Mali | Bamako | Sojoji | Rasha | Wagner | Faransa
Bayan yanke alaka da Faransa, Mali ta yi maraba da sojojin hayar Wagner na RashaHoto: French Army /AP/picture alliance

Ukraine ta bayyana matakin na Mali da cewa abin takaici ne, kuma ba a yi hangen nesa ba. Kakakin gwamnatin Mali Kanar Abdoulaye Maiga wanda ya ba da sanarwar katse huldar diflomasiyya tsakanin Mali da Ukraine din, ya zargi Kyiv da hannu a harin da aka kai Malin. Ya bayar da misali da ikrarin da wani jami'in leken asirin Ukraine Andriy Yusov ya yi, wanda ya amince da hannun Ukraine a abin da Maiga ya baiyana a matsayin ragwanci da cin-amana da kuma harin dabbanci na kungiyoyin 'yan ta'adda. Ma'aikatar harkokin wajen Ukraine din dai ta soki hukuncin gwamnatin ta Mali a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Internet, tana mai cewa babu wata hujja da aka bayar da ya nuna gwamnatin Kyiv ta taka rawa a harin kuma gwamnatin Mali ba ta yi wani cikakken bincike game da lamarin ba.

Karin Bayani: Rasha ta bai wa Burkina Faso alkama

Harin da ake magana a kansa dai ya faru ne a karshen watan Yulin da ya gabata a arewacin yankin Kidal, kuma lamarin ya haifar da damuwa da fargabar yaduwar rikicin Rasha da Ukraine a Afirka. A cewar 'yan tawayen Abzinawa, dauki ba dadi da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a kauyen Tinzaouatene da ke kan iyaka da Aljeriya ya halaka sojojin Mali 47 da sojin hayar Rasha  na Wagner 84 da kuma karin wasu mutane 80 da ke da alaka da kafofi dabam-dabam da sojojin na Wagner. Harin dai na zama mafi muni da Rasha ta fuskanta kawo yanzu, a kasar da ke yankin yammacin Afirka. Wannan lamari a cewar Abdoul Sogodogo mai nazari kan al'amuran siyasa a Malin, na nema ya lalata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Mali | Bamako | Zanga-Zanga | Rasha | Wagner
Al'ummar MAli dai, sun yi maraba da sojojin hayar Rasha na Wagner da ke kasarsuHoto: Florent Vergnes/AFP/Getty Images

An dai dauki kusan makonni biyu kafin hukumomin Mali su zargi Ukraine game da harin, inda suka yi ikirarin cewa Yusov na hukumar leken asirin sojan Ukraine ya bayyana a gidan talabijin din kasarsa a makon da ya gabata ya kuma amince da hannunsu a harin yana cewa maharan sun samu cikakkun bayanai da suka taimaka musu samun nasarar kai hari kan 'yan ta'adda na Rasha 'yan Ina da yaki. Sanarwar gwamnatin Mali dai na da tasiri a siyasar kasar musamman ta la'akari da yadda ofishin jakadancin Ukraine a birnin Dakar na Senegal da ya nuna goyon bayansa ga harin na arewacin Mali, ya goge sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Karin Bayani: Yara za su shiga halin tasku a kusurwar Afirka

Wannan ya sa gwamnatin Senegal ta kira jakadan Ukraine din, domin ya yi mata karin bayani. Tuni dai wani hoto na mayakan Abzinawa dauke da tutar Ukraine, ya bayyna a shafukan Internet. A dangane da wannan dambarwa dai, manazarta kamar Abdoul Sogodogo mai nazari kan al'amuran siyasa a Mali na ba da shawarar a kai zuciya nesa. Yayin da halin da ake ciki a Mali ka iya zama wani fage na ci gaban yakin Rasha da Ukraine, illar da hakan zai iya haifarwa ga kasar na da yawa. Kasancewar sojojin Wagner da kuma zargin shigar jami'an leken asirin Ukraine, na iya yin tasiri a kan muradun kasashen waje da al'amuran cikin gida na kasar Mali.