1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin hayar Rasha da dama a Mali

July 30, 2024

Wasu mayakan tawaye masu alaka da al-Qaeda a Mali, sun kai hari kan sojojin kamfanin Wagner a iyakar Mali da Aljeriya. Lamarin ya haddasa asarar mayakan na haya da dama.

https://p.dw.com/p/4it9l
Yadda ake kwashe gawarwakin sojojin Wagner
Yadda ake kwashe gawarwakin sojojin WagnerHoto: Marina Lystseva/REUTERS

Gomman sojojin haya mallakin kamfanin Wagner na kasar Rasha ne rahotanni ke tabbatar da cewa mayaka masu ikirarin jihadi suka kashe a yankin arewacin Mali.

Wannan dai al'amari ne da masu sharhi kan al'amuran tsaro ke bayyana shi da cewa bala'i mafi muni da sojojin na haya suka gani cikin shekaru.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa baya ga wadanda suka mutum, 'yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu sojojin na Wagner biyu.

Kiyasin da aka yi dai, ya nuna sojojin na haya akalla 50 ne ke tafiya cikin ayari da suka gamu da mayakan masu alak da kungiyar al-Qaeda a iyakar Malin da kasar Aljeriya.

Wani faifan bidiyo ne dai ya nuno adadin da masu sharhi kan tsaron suka fitar a harin da ya auku a karshen makon jiya.