1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kashe 'yan bindiga akalla 100 a arewacin Najeriya

October 14, 2023

Sojoji a Najeriya sun yi luguden wuta ta sama a kan 'yan bindigar daji da ke addabar jama'a a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4XWv8
Sojojin Najeriya cikin aikin sintiri
Sojojin Najeriya cikin aikin sintiriHoto: AFP/Getty Images

A ranar Talatar da ta gabata ne dai sojojin sama na Najeriyar suka tsananta hare-hare a dazukan jihar Zamfara, kuma kamar yadda kakakin rundunar mayakan saman kasar ke cewa ba su ma kai ga tantance adadin 'yan bindigar da suka kashe ba.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce hare-haren na sojojin na Najeriya sun kashe akalla 'yan bindigar mutum 100.

Tsawon shekaru ne dai yankunan arewa maso yammacin Najeriya da ma tsakiyar kasar ke fama matsalar 'yan bindiga da ke satar mutane domin karbar kudaden fansa.

Daga cikin wadanda suke sacewa ma har da dalibai a makarantunsu manya da kuma kanana.

Ko a 'yan kwanakin nan ma dai 'yan bindigar sun kwashi daliban jami'o'i na arewacin Najeriyar.