1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun garkuwa da jama'a a Kaduna

Abdoulaye Mamane Amadou
June 20, 2022

'Yan bindiga sun kaddamar da jerin hare-hare a wasu sassan jihar Kaduna a Najeriya tare da garkuwa da mutane ciki har da mabiya addinin Kirista.

https://p.dw.com/p/4Cxz0
Nigeria Nach Massenschießerei in der Kirche
Hoto: Amaka Okoye/DW

Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka mutane uku, tare da yin garkuwa da wasu 36, a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso yammacin Najeriya. 

Kwamishinan tsaron cikin gidan jihar kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da harin, sai dai yace jami'an tsaro na cigaba da kokarin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Harin na zuwa ne kwanaki bayan wani harin ta'addancin da 'yan bindiga suka kai kan mabiya addinin Kirista da ke tsaka da ibada a yankin Kudu maso yammacin Najeriya, inda aka kashe mutun 40.