1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Shugaba Maduro zai karbi sakamakon zabe da hannu bibbiyu

July 28, 2024

Kusan masu zabe miliyan 21 ne suka yi rejista domin kada kuri'a a zaben da ya ke gudana ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/4iq8o
Mai zabe a Venezuela
Mai zabe a VenezuelaHoto: Ariana Cubillos/AP Photo/picture alliance

Al'ummar kasar Venezuela na kada kuri'a a zaben shugaban kasa wanda sakamakonsa ka iya kawo sauyi a cikin shekara shida ko kuma ci gaba da manufofin shugaba Nicolas Maduro.

Duk wanda ya lashe zabe tsakanin Mista Maduro da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon ma'aikacin diflomasiyya  Edmundo Gonzalez, nasarar za ta yi tasiri a nahiyoyin Amurka.

Rikici tsakanin Trump da Maduro

Magoya baya da kuma 'yan adawar gwamnati da dama sun nuna alamar tserewa daga kasar su shiga kasashen duniya don neman damarmaki. A halin yanzu akwai 'yan Venezuela sama da miliyan 7.7 da suke kasashen ketare.

Tawagar kwararrun zabe za ta je Venezuela

Babban abokin hamayyar Maduro Mista Gonzalez ya sha alwashin bibiyar yadda zaben ke gudana domin tabbatar da an yi adalci.