1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka tana neman a hukunta Nicolas Maduro

Abdourahamane Hassane
March 27, 2020

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya mayar da martanin cikin fushi bayan da Amirka ta zargeshi da yin safarrar miyagun kwayoyi.

https://p.dw.com/p/3a8bV
Venezuela Präsident Nicolas Maduro
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Delacroix

Maduro ya bayyana Shugaban na Amirka Donald Trump a matsayin dan nuna wariyar launin fata wanda ya ce ya kulla masa sharri. A lokacin da yake yin wani taron manema labarai ministan shari'a na Amirka Bill Barr ya ce za su ba da ladan dala miliyan 15 kyauta ga duk wanda ya ba da bayyanan da za su taimaka a kai ga kama Maduro domin ya gurfana a gaban shari'a a Amirkar.