1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar yan sanda ta janye gayyatar Bukola Saraki

Uwais Abubakar Idris
June 4, 2018

Rundunar yan sandan Najeriya ta ce yanzu ba sai Sanata Bukola Saraki ga baiyana a gabanta ba, abin da ta ke bukata shi ne ya bada bayani a rubuce cikin sa'oi 24.

https://p.dw.com/p/2yvht
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki yace ya sami sanarwa daga rundunar yan sandan Najeriyar cewa a yanzu bata bukatar ya baiyana a gabanta domin amsa tambayoyi sai dai kawai ana bukatar ya yi bayani a rubuce cikin sa'oi 24 game da abin da ya sani kan zargin cewa yana da hannu a mummunan fashi da makami da aka yi a garin Offa a jihar Kwara a watan Afirilu. Tuni dai shugaban majalisar dattijan yace a shirye yake ya yi hakan.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Hoto: DW/U. Musa

Tun da farko dai gayyatar da rundunar ‘yan sandan ta yiwa Sanata Bukola Saraki na nuna kara jan layi yayin da guguwar siyasar da ke kadawa a tarayyar Najeriyar, bisa dagewar da ta yi cewa  shugaban majalisar dattawan na da tambayoyin da zai amsa mata, saboda biyar daga cikin mutane 22 da aka kama da zargin hannu a mumunan fashi da makami da aka yi a garin Offa sun bayyana alaka da shugaban majalisar dattijan da kuma gwamnan jihar Kwara.

Munin harin na ranar 5 ga watan Afrilu ya yi sanadiyyar kashe mutane 33 ciki har mata masu ciki abinda ‘yan sanda suka dage da cewa akwai dalilai da suka sanya su gayyatar shugaban majalisar. Mr Moshood Jimoh shi ne kakakin rundunar yan sandan Najeriya.

‘’Rundunar ‘yan sanda na gayyatar shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki da ya kawo kansa ofishin yan sanda da ke unguwar Guzape a Abuja, domin ya amsa dukkanin zarge-zargen da ake masa da wadanan gungun ‘yan fashi suka yi a Offa, inda suka kashe mutane 33 da ‘yan sanda 11. Rundunar yan sandan Najeriya zata tabbatar da bin doka da yiwa duk wani mai laifi adalci’’

Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Tun kafin wannan lokaci dai shugaban majalisar dattawan ya bara kan cewa ‘yan sandan na neman shafa mashi kashin kaji a kan abinda baya da alaka da shi.

Sanin cewa Sanata Bukola Saraki shine mutum na uku a majalisar da ‘yan sandan suka yiwa irin wannan gayyata bisa zargi iri daban daban, kama daga Sanata Shehu Sani da Senata Dino Melaye da karara ke sukar gwamnati ya sanya yiwa lamarin kallo da dalilai na siyasa. Comrade Isa Tijjani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum yace akwai bukatar fayyace lamarin.

Tuni dai shugaban majalisar dattijan yace zai amsa gayyata don bada amsa ga tambayoyin da za’a yi mashi, sai dai raba al’amarin da siyasa na da kamar wuya musamman sanin cewa Sanata Sarakin na cikin yayan jamiyyar sabuwar PDP da ke barazanar ficewa daga jamiyyar APC mai mulki.