1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rashin tsaro a Sahel karkashin gwamnatocin soji

September 13, 2023

Yanayin tsaro a Sahel ya na kara tabarbarewa sakamakon yawaitar juyin mulkin soji a yankin. Masana sun ce komawa mulkin dimukuradiyya ne kadai zai magance matsalar.

https://p.dw.com/p/4WI9D
Yaki da mayakan jihadia a yankin Sahel
Yaki da mayakan jihadia a yankin SahelHoto: Inside the Resistance

Masana a yankin Sahel na ci gaba da kokawa kan tabarbarewar tsaron a yankin da ya dade ya na fuskantar tashe-tashe hankula, sai dai har yanzu an gaza magance matsalar duk da sojoji da suka kwace iko da wasu kasashen yankin. Tuni dai gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen arewacin Mali suka sha alwashin shiga yaki da gwamnatin mulkin sojin kasar. 

Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a Mali dai na zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan. A yawancin lokuta suna kai hare-haren ne a yankin arewacin kasar da ke yankin Sahel. Rundunar Sojin Mali ta tabbatar da mutuwar dakarunta a kalla 10 a wani harin da 'yan bindiga suka kai yankin Gao.

Karin Bayani: Nijar ta cimma yarjejeniya da makwabtanta

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce wasu jami'an soji 13 sun jikkata. Ko a makon da ya gabata an kai wasu tagwayen hare-hare da suka salwantar da rayukan gomman fararen hula da kuma sojojin gwamnati. Masu sharhi a Mali irinsu Dr Shaantanu Shankar na ganin fara janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar na da alaka da kara tabarbarewar tsaron a yanzu.

Filmstill Dokumentatio Terror im Sahel - Kampf gegen die Dschihadisten
Hoto: Inside the Resistance

"A yanzu haka, ana kai hare-hare arewacin Mali ne, kuma a nan ne yawanci dakaruun Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya suka fi mayar da hankali a kai. Dama dai, tashe-tashen hankula sun samo asali ne daga arewacin Mali din."

A yanzu haka, wata tsohuwar gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen kasar ce ta dauki alhakin kai wani harin garin Bourem da ke yankin Gao da ta ce ta kwace ikon wasu sassan garin. Ana dai ganin cewa, idan gwamnati bata dauki kwakwarar matakin kakkabe 'yan bindigan ba, matsalar tsaro ka iya ta'azzara. Mutaru Muumuni, masanin tsaro ne da ke zaune a kasar Ghana ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki mataki domin jama'a su samu kwanciyar hankali a yankin.

"Wannan shekarar, ka iya kasancewa mafi hatsari kuma mafi munin ayyukan ta'addanci a yankin yammacin Afirka."

Ko a makon da ya gabata, sojoji kimanin 40 ne aka kashe a Burkina Faso a wani hari yayin da a Nijar, bayan da sojoji suka yi juyin mulki an samu karuwar hare-haren 'yan bindiga kan fararen hula, wanda yawancin 'yan kungiyar JNIM da ke da alaka da al-Qaeda ta ke kaiwa. Wasu dai na ganin matsalolin tsaron suna kuma da alaka da dambarwar siyasar da ake fuskanta a yankin, musamman ma da sojoji ke kwace iko da wasu kasashen yankin. Bram Posthumuus, dan jarida ne mai zaman kansa a yammacin Afirka.

Filmstill Dokumentatio Terror im Sahel - Kampf gegen die Dschihadisten
Hoto: Inside the Resistance

"Kamar yadda aka sani, juye-juyen mulkii baya samar da zaman lafiya sai dai dagula lissafin al'amura."

Muntaru Mumuni, na ganin mayar da kasashen da suka fuskancin juyin muulki kan tafarkin dimukuradiyya zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro.

"Tun da fari, akwai bukatar a mayar da mulkin dimukuradiyya a yankin. Kuma abun da na ke nufi shi ne, mu samar da shugabanci domin ci gaban al'umma ba domin neman iko ba. Mu kuma tabbatar da cewa mun gina shugabancinmu kan sauke nauyin al'ummar da suka rataya a wuyanmu. Mun ga rashin adalci da cin hanci da rashawa da kuma taka doka."

Ana dai ganin yanzu 'yan tawayen sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2015 da suka cimma da hukumomin Mali.