1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa kungiyar tawaye da sojoji a Nijar

August 9, 2023

Tsohon jagoran 'yan tawayen Abzinawa na Nijar, Rhissa Ag Boula ya sanar da kafa wata kungiyar tawaye da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

https://p.dw.com/p/4UxLl
Niger | Zanga zangar adawa da takunkumi kan Nijar
Hoto: Balima Boureima/REUTERS

A cikin sanarwar da Rhissa Boula ya fitar, ya ce manufar kafa kungiyar mai suna CRR ita ce, fafatukar sake mayar da shugaba Mohammed Bazoum kan karagar mulkin kasar da sojoji suka hambarar kuma suke ci gaba da tsare da shi.

Kungiyar ta CRR ta ce ta na goyon bayan kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa da ke neman mayar da Nijar kan tafarkin dimukuradiyya.

Kafa sabuwar kungiyar tawayen ta Abizinawa na zuwa ne bayan da majalisar mulkin sojin kasar ta ki yin maraba da tawagar  jami'an diflomasiyya na kungiyar ECOWAS da AU da Amurka da suka je kasar a baya-bayan nan.