1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Gomman rayuka sun mutu a harin ta'addanci

September 8, 2023

Rahotanni daga Mali sun yi nuni da cewa, a kalla mutane 64 aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da aka kai sansanin soji da kuma wani jirgin ruwan a kogin River.

https://p.dw.com/p/4W63J
Hoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Ana dai zargin 'yan ta'addan da kai mabambanta hare-haren ne kan wani jirgin ruwa a kusa da Timbuktu da kuma sansanin soji da ke Bamba a arewaci yankin Gao.

Hukumomi Mali sun ce harin ya salwantar da rayuwar fararen hula 49 da kuma jami'an soji 15.

Karin bayan:'Yan jihadi sun halaka mutum guda a Timbuktu

A cewar gwamnatin kasar, kungiyar nan ta masu tsattsauurar ra'ayin addini ta JNIM da ke da alaka da al-Qaida ne suka dauki alhakin kai hare-haren.

Tun dai a karshen watan Augustan shekarar 2023 ne kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai suka doshe hanyoyin birnin Timbuktu yayin da rundunar sojin Mali ta tura da dakarunta yankin, inda suka hana kai kayan abinci zuwa birnin da ke a hamadar sahara.