1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: An kama gomman mutane bayan mutuwar Navalny

February 17, 2024

Masu rajin kare hakkin bil Adama a Rasha sun ce an kama fiye da mutane 100 a kasar yayin da ake ci gaba da makokin jagoran adawar kasar Alexei Navalny. wanda ya mutu a gidan yari.

https://p.dw.com/p/4cWfq
Hoto: Peter Kneffel/dpa/picture alliance

Wata kafar yada labarai ta internet ta kasar ovd.info ta ruwaito cewar a birnin St Petersburg kadai, an kama mutum fiye da 60 sakamakon sanar da mutuwar Navalny da ya yi kaurin suna wajen caccakar lamirin gwamnatin shugaba Putin. Faya-fayan bidiyo da aka wallafa sun kuma nuna yadda jami'an 'yan sandan ke kama wadanda suke aje furanni da kuma kunna kyandira domin nuna alhinin mutuwar Navalny.

A share guda, gwamnatin Birtaniya ta gayyaci jami'an diflomasiyyar Rasha domin tabbatar da cewa sun daura alhakin mutuwar Navalny kan hukumomin Rashaalhakin mutuwar Navalny kan hukumomin Rasha

A birnin Landan, gomman mutane ne dauke da kwalaye suka yi jerin gwano a gaban offishin jakadancin Rasha  suna cewa, a dakatar da kisan gillar da Putin ke yi. Kasashen yammacin Turai dai na ci gaba da yin Allah-wadai tare da daura alhakin mutuwar madugun adawan kan shugaba Vladmir Putin.