1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daurin shekaru 19 ga Navalny a Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 4, 2023

Babban mai sukar mahukuntan Rasha Alexei Navalny da kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 19 a gidan kaso, ya bukaci al'ummar kasar da su ci gaba da nuna turjiya ga fadar Kremlin.

https://p.dw.com/p/4Una2
Rasha | Alexei Navalny | Hukunci | Shekaru 19
Babban mai adawa da gwamnatin Moscow Alexei NavalnyHoto: EVGENIA NOVOZHENINA/REUTERS

Alexei Navalny ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a kafar sadarwa ta Facebook jim kadan bayan da aka yanke masa hukuncin, yana mai cewa mahukuntan na son firgita al'ummar da ke nuna turjiya a gare su ne. Tuni dai Amurka ta bayyana takaicinta kan wannan hukunci da aka yanke wa Navalny a wata sabuwar tuhuma da aka yi masa, tana mai bayyana shi da hukuncin rashin adalci da aka yanke a shari'a ta rashin adalci.