1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ya mutu a kurkuku

February 16, 2024

Hukumomin gidan kurkukun yankin Artic mai tsananin sanyi da ke wajen birnin Moscow, sun sanar da mutuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny, bayan ya yi tattaki kafin daga bisani ya fita daga cikin hayyacinsa.

https://p.dw.com/p/4cU7u
Alexei Navalny
Alexei NavalnyHoto: Pavel Golovkin/AP Photo/picture alliance

Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny, da ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Vladimir Putin, na fuskantar daurin shekaru 19, bisa zargin aikata laifin cin hanci da rashawa da kuma kiran gangamin adawa da manufofin fadar Kremlin.

 A watan Disambar 2023, aka maida Jagoran adawar wani gidan yarin da ke yankin Artic mai tsananin sanyi da ke da nisan kilomita 1,900 daga birnin Moscow.

Tuni dai kasashen duniya suka fara martani kan mutuwar Alexei Navalny, shugaban kasar Latvia da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bayyana mutuwar Navalny a matsayin kisan gillar da fadar Kremlin ta yi.