1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

NNPCL ya fara dakon mai daga matatar Dangote

Binta Aliyu Zurmi
September 15, 2024

Matatar mai ta Dangote a Najeriya ta fara lodin man fetur ga motocin kamfanin mai na kasa NNPCL. Matatar mai ta Dangote ta wallafa wani bidiyo da ke nuna jerin motocin kamfanin NNPCL a harabar matatar.

https://p.dw.com/p/4keFr
Nigeria Tankstelle in Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Wannan shi ne karon farko da kamfanin na NNPCL ke daukar mai daga matatar ta Dangote, bayan daukar lokaci ana kokarin cimma matsaya a kan batun cinikin danyen mai.

Motocin dakon mai kusan 500 ne rahotanni suka tabbatar sun yi jerin gwano a harabar matatar, suna jiran daukar man fetur din ya zuwa kasuwa a Najeriya.

Daga ranar 1 ga watan Oktoba mahukunta a Najeriya sun ce kamfanin NNPCL zai fara bayar da gangar danyen mai 385 a duk rana domin tace shi daga matatar ta Dangote.

Ana fatan wannan matakin ya kawo karshen matsalar karancin mai da ma tsadarsa a Najeriya, kasar da ke da dimbin arzikin man fetur amma tun bayan janye tallafi mai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ya saka al'ummar kasar cikin wani mawuyacin hali.