1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokoki za ta sasanta Dangote da NNPCL

July 23, 2024

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan lamarin Ikenga Ugochinyere ya sanar a ranar Litinin da daddare cewa kwamitin nashi zai duba zargin da ake wa kowane bangare a tsakanin masu takaddamar.

https://p.dw.com/p/4icA3
Hoto: Christophe Petit Tesson/picture alliance/dpa

Majalisar dokokin Najeriya ta kaddamar da bincike kan zargin shigo wa kasar da gurbataccen man fetur, a wani mataki na shawo kan takaddamar da ta kunno kai tsakanin sabuwar matatar man fetur mallakin attajirin nan Aliko Dangote da jami'an gwamnatin da ke kula da bangaren man fetur na kasar.

Wasu jami'an gwamnati sun zargi Dangote da yunkurin mamaye harkar fetur shi kadai alhali fetur din da yake son fara fitar a Najeriya ba shi da inganci, yayin da attajirin ya nesanta kansa da zarge-zarge, lamarin da ya haifar zazzafar takaddama da ta fara fitowa bainar jama'a a 'yan kwanakin nan.

Sai dai ma'aikatar kula da man feur ta kasar ta ce ganawar dabangarorin biyun suka yi a ranar Litinin da daddare ta bude kofar samun maslaha.