1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Shekaru 63 da zama Jamhuriya

Salissou Boukari RGB
December 20, 2021

Cikin yanayi na kalubalen tsaro al'ummar Jamhuriyar Nijar suka shiga gudanar da shagulgulan bukukuwan ranar da kasar ta zama Jamhuriya shekaru 63 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/44VUW
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

A wannan Asabar jama'a a Jamhuriyar Nijar suka shiga gudanar da shagulgulan bikin tuna ranar da kasar ta zama Jamhuriya shekaru 63 da suka gabata. Albarkacin wannan rana kamar yadda wakilinmu na Yamai Salissou Boukari ya rawaito mana, shugaban kasar, Mohamed Bazoum, ya yi jawabi ga 'yan kasar inda a tsawon mintuna akalla 24 ya tabo fannoni da dama masu mahimmanci.

Karin Bayani: Shekaru 61 da samun 'yancin kai a Nijar

Kama daga na tsaro da kiwon lafiya da Ilimi da yaki da cin hanci, da kuma batun mayar da 'yan gudun hijira ya zuwa gidajensu a yankin Diffa. Sai dai kan batun tsaro shugaban ya kara jaddada bacin ransa ga masu nuna adawa da kasancewar sojojin kasashen waje a kasar ta Nijar yana mai cewa “Mun bai wa batun horas da sojojinmu babban mahimmanci ta yadda za su iya fuskantar babban kalubalen da ke gabanmu na tsaro, don haka wadanda ke nuna adawa da wannan yarjejeniyar ban san ko sun gane cewa sun zamana tamkar kawayen 'yan ta’addan wadanda su daman ba sa fatan sojojinmu su samu horon da za su iya kalubalantarsu.”

Niger 61. Jahrestag  | Militär
Nijar na fama da matsalar tsaroHoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

Shugaban Bazoum ya jinjina wa sojojin kasar ta Nijar, bisa jan kokarin da suke na yakar 'yan ta’adda, kafin daga bisani ya jinjina wa kasashen da ke tallafa wa kasar ta Nijar a fannin tsaro kamar kasashen Amirka da Faransa da Jamus da Beljiyam da Kanada da kuma Italiya. Sannan daga karshe, ya yi kira ga 'yan kasar ta Nijar da su yi allurar riga-kafin cutar corona domin a samu galaba kan wannan cuta da ta addabi duniya. Ana dai wannan biki a duk ranar 18 na watan Disambar kowacce shekara tun bayan da tsohon Shugaban kasar Tanja Mamadou ya kirkiro ta a shekarar 2006.