1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bude makarantar horon manyan sojoji

Gazali Abdou Tasawa ATB
October 15, 2021

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya ce girka makarantar horon manyan sojoji a Nijar zai taimaka wa kasar domin tunkarar kalubalen 'yan ta’adda.

https://p.dw.com/p/41kZb
Niger Militär
Hoto: Gazali Abdou

Sojoji ofisa-ofisa guda 22 daga rundunar soja ta kasa wato FAN na daga cikin rukunin farko na daliban makarantar horas da manyan sojoji a Nijar,. Akwai kuma ofisan jami’an jandarma guda biyu da kuma ofisoshin soja guda biyu na rundunar Garde Nationale.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan biki, shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bayyana cewa girka wannan makaranta zai taimaka wa Nijar din tunkarar kalubalen 'yan ta’adda da take fuskanta.

Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

"A tsawon shekaru 10 da muke yaki da ta’addanci, mun karfafa matakan inganta ayyukan rundunar sojojin kasarmu. Mun kashe kudade masu yawa wajen aikawa da manyan sojojinmu zuwa samun horo a ketare. Yanzu da muka girka wannan makaranta tamu, za mu horas da sojoji ba tare da kashe kudade masu yawa ba, sojojin da kuma za su shugabanci manyan barikokokin sojan da kuma manyan rundunoni da bataliyoyin sojan da ke kula da tsaron kasarmu."

Daga nasa bangare shugaban babbar makarantar horas da manyan sojojin da aka bude, Kanal Abdourazak Ben Ibrahim, ya ce da wannan makaranta sojojin Nijar ba za su yi kasa a gwiwa ba a fagen yaki.

Niger Militär
Hoto: Gazali Abdou

"Wani karin magana na cewa kintsa manyan sojoji shi ne shiryawa yaki. Da haka horon da manyan sojojin Nijar za su samu a wannan makaranta, zai shirya su ga iya tunkarar salon yaki irin na wannan zamani ta hanyar horas da su kan irin sarkakiya da siddabaru da ke tattare da shi, da kuma nakaltar yadda ake sarrafa makamai da na’urorin yaki na zamani, da iya ci gaba da jan daga ko a cikin wani hali suka kasance."

Shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ya yi amfani da wannan dama ta bude wannan makaranta wajen gabatar da siyasarsa kan harkokin tsaro wacce ta tanadi bude wasu sabbin makatantun horas da sojoji da kuma kara yawansu.

An yi ta dai rera wakoki na tayar da tsumin sojoji a wajen wannan biki wanda ya samu halartar rundunoni dabam-dabam na jami’an tsaron kasar ta Nijar.