Shekaru 61 da samun 'yancin kai a Nijar
August 3, 2021Bisa al’ada a jajibirin ranar shugaban kasar ke gabatar da jawabi ga ‘yan kasa da ake kira “message à la Nation”, jawabin da ke tabo batutuwa masu mahimmanci game da rayuwar ci gaban kasa.
A daren Talatar ma dai shugaban kasar Bazoum Mohamed, ya yi jawabin da ya dauki hankulan ‘yan kasar, inda a bana Damagaram ke karbar bakuncin bikin a matakin kasa.
Jim kadan da kammala jawabin masana tsirrai ta bakin Kanar Sani Ado mai ritaya ya ce maye shuka itatuwan zogale abun dubawa ne.
Kamar ko wace shekara dai a irin wanan rana ta zagayowar tuni da samun ‘yan cin kai ‘yan kasar ke bayyana ra’ayoyi a kan batutuwan da suka shafi kasarsu ta gado.
Wasu daga cikin su sun yaba da tafiyar gwamnati kasar wacce ba ta jima da kama mulki ba, yayin kuma da wasu ke cewa lallai ne a sake lale na daga tafiyar siyasar kasar da kullum ke jiya i yau.