1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula a zanga-zangar Najeriya

Muhammad Bello LMJ
August 6, 2024

Da alama zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa a Najeriya, ta sake rincabewa a Fatakwal babban birnin jihar Rivers bayan dan lafawar da ta yi.

https://p.dw.com/p/4jAxp
Najeriya | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa |
Zanga-Zanga kan tsadar rayuwa, na ci gaba da gudana a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Masu zanga-zangar sun yi ta shelar kashedi musamman ga masu manyan katuna da kanana kan su tabbatar ba su bude ba, inda kuma suka fantsama kan titunan birnin suna kururuwar cewar dole Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauka tare da babbale wasu manyan alluna da ke dauke da fastocin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar. Ana tsaka da zanga-zangar gama-garin ne kuma aka samu daukewar wutar lantarki a fadin kasar, a daidai lokacin da aka shiga rana ta shida ta zanga-zangar ta neman sauyi a Najeriyar. Matasa a jahar Rivers mazansu da matansu sun sake fita kan titunan birnin wato Fatakwal, domin neman gwamnatin Tinubu ta saurari kokekoken jama'ar kasar kan tsananin yunwa da tsadar rayuwa da ke gallabar su.

Najeriya | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa | 'Yan Sanda | Kisa
Zargin jami'an 'yan sanda da yin amfani da karfin tuwo a kan masu zanga-zangaHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Tuni dai aka fara barnata wasu kayayyaki, musamman wadanda ke kan tituna. Zanga-zangar a sauran jahohin yankin Niger Delta  kusan za a iya cewa ba ta yi tasirin da iyayen zanga-zangar na kasa suka yi fata ba, illa a jihar Delta da a ka yi ta samun dauki ba dadi da jami'an tsaro. Ko da yake yankin Igbo ya zabi kauracewa zanga-zangar, gwamnatocin jihohin su wato Abia da Ebonyi da Anambara da Imo da Enugu sun koka ne da cewar maimakon ma'aikatan gwmnati su fito bakin aiki sai kawai suka ci gaba da zaman dirshan a gidajensu. Kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta IPOB ma, an nunar ta dada assasa umarnin na zaman dirshan a gida a fadin yankin na Igbo.