1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Laifin ta'adda ga masu kai hari a Kudu maso gabas

June 8, 2021

A yayin da ake ci gaba da kokarin kwantar da hankula a sashen Kudu maso gabashin Najeriya da ke fama da tashin hankali, gwamnatin kasar ta ce za ta ayyana masu kona kadarorinta a matsayin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/3ubYa
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Ya zuwa ranar Talatar nan dai akalla 'yan sanda 78 da soja 38 ne dai aka hallaka a jihar Imo da ke zaman cibiyar ta da kayar bayan kungiyar awaren IPOB, ko bayan kona ofisoshin 'yan sanda da hukumar zabe.

To sai dai kuma ita ma Abujar na mayar da martani da karfi na hatsin da ya kai kisa da kama da dama na 'ya'ya na kungiyar a daukaci na jihohin yankin na Kudu maso gabas.

Kuma ko bayan nan dai tarrayar Najeriyar ta ce tana shirin gurfanar da masu kona kadarori na hukuma a kasar a bisa laifi na ta'addanci.

Karin bayani: 'Yan sandan Najeriya sun kame 'yan IPOB

Kama daga masu karya layin dogo ya zuwa masu kona ofisoshin 'yan sanda da hukumar zabe dai ministan labarai na kasar Alhaji Lai Mohammed ya ce hukunci na kisa na shirin ya hau duk masu kokari na rusa dukiyar al'umma a kasar.

To sai dai kuma gwamnan jihar ta Imo da ke ji har a kwakwalwa a kokari na ta da kayar bayan dai ya ce dole ne a mutunta kadarori na gwamnatin kasar da ma mutuncinta.

Hope Ozudinma da ya gana da shugaban kasar domin ba shi bayanin ci-gaba da ke cikin yankin yanzu ya ce dole ne shugabannin yankin su tashi tsaye tare da aiki da gwamnati domin samar da tsaro a cikin wannan yanki.

Karin bayani: Najeriya: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari

"Batu ne na sanin wannan kadara ce ta gwamnatin tarrayar sannan kuma ka tashi ka lalata ta da niyya. Abun da kake yi shi ne kokari na lalata makoma ta kasa, kuma bai kamata mu kyale wannan ba. Koma mene ne matsayi na gwamnati ina ji akwai abubuwa guda biyu, ko dai ka mutunta gwamnati ka kyale mata kadara, ko kuma ka lalata kadara ka fuskanci fushi na hukuma."

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma (a tsakiya) a ziyarar gani da ido bayan wani hari da aka kai kan hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Owerri a farkon watan Afrilun 2021
Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma (a tsakiya) a ziyarar gani da ido bayan wani hari da aka kai kan hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Owerri a farkon watan Afrilun 2021Hoto: David Dosunmu/AP/picture alliance

"Saboda haka babu batu na yaudara a tunanin komai na tafiya dai-dai, komai fa a lalace yake. Dole ne shugabanni su tashi domin tabbatar da aiki da gwamnati domin samar da zaman lafiya. A jihar Imo ni kadai ba zan iya tabbatar da tsaro ba. Dole ne in yi aiki da sarakuna na gargajiya , da shugabannin al'umma da matasa, domin ganin an samu zaman lafiya."

"Sai ka ji wasu sun zo daga wajen jihar da sunan 'yan bindigar da ba a sansu ba. To yaushe ne za a sansu. Kuma ka ji sun aikata ta'annati sun tsere."

To sai dai in har Abujar na shirin taunin tsakuwar da nufin aiken sako ga aya, daga dukkan alamu hada kai da masu siyasar yankin na zaman kalubale da ke da girman gaske.

Zanga-zangar 'yan rajin kafa kasar Biafra a shekarun baya a birnin Aba
Zanga-zangar 'yan rajin kafa kasar Biafra a shekarun baya a birnin AbaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Da dama a ciki na shugabannin yankin dai sun zabi karatun kurma ko dai a bisa tsoro ko kuma goyon baya ga masu ta da kayar bayan da burin ke kara karkata zuwa ga siyasa maimakon a waren dauri.

Kabiru Adamu dai na zaman mai sharhi a cikin harka ta tsaro da kuma ya ce kara karfi na hatsi a cikin yankin na iya karewa da kara yamutsa lamura maimakon kwantar da hankulan da ke zaman babban burin kowa.

Manyan hafsoshin tsaro na tarrayar Najeriya dai sun share wunin wannan Talata suna wata ganawar sirri bisa rashin tsaron da ke dada rikida ya zuwa gwagwarmayar neman mulki na kasar a nan gaba.