1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kara kudin fiton kananan motoci

July 4, 2022

Gwamnatin ta ce karin wani kokari ne na kauce wa yawan matattun motoci, kuma ta tanadi biyan kudin fito bai daya ga duk wata motar da ba ta wuce shekara ta 2013 da kerawa ba.

https://p.dw.com/p/4DeBL
USA Pontiac Autofriedhöfe
Hoto: picture-alliance/dpa/ZUMA Wire/J. West

Kafin yanzu dai duk wani mai fatan shigo da kananan motoci irin su Golf ko Vectra koma duk wata karamar mota ta hawa ko kuma haya dai to ya kan tanadi abun da ke tsakanin Naira dubu 500 zuwa 600 kan kowacce. To sai dai kuma a karkashin wani sabon tsarin da gwamnatin kasar ta fitar dai kudin fiton ya haura ya zuwa Naira miliyan daya da kusan dubu dari uku ko kuma karin kaso 120 cikin dari na kudaden baya.

Tuni dai karin ya fara jawo dagun hakarkari cikin masana'antar tsofoffin motocin da dubban matasa ke dogaro a kanta domin harkoki na rayuwa. Abubakar Gidado Adams daya ne a cikin shugabannin dillallan tsofoffin motoci a Abuja, da kuma ya ce cinikin motocin na fuskantar barazana mai girma.

"Golf in ka samu wagon din ta miliyan biyu da dari biyar ne, ita kuma Toyota Pencil miliyan uku da dari biyar ce. Ita Toyota wadda ake kabu-kabu da ita a cikin gari yanzu ta kai miliyan hudu, in kuma ka samu 2010 dinta ta kai miliyan hudu da dari takwas, to ina za mu kai wannan. Kuma in ka je tashar jirgin ruwan ba motocin saboda in ka sawo mota sai ka sai da guda uku za ka sayi daya, gaba aka ci ke nan ko baya? Doka ce aka ce an bai wa kwastam damar kama mota ko a karkashin gado take in bata biya kudin fito ba. Ita kuma dokar ba ta Kur'ani ba ce ko kuma Bible, balle a ce in an gyara ta za a samu matsala a duniya.”

USA Pontiac Autofriedhöfe
Hoto: picture-alliance/dpa/ZUMA Wire/J. West

Kokari na gyaran doka ko kuma sabon rikici na tattalin arziki dai, ko bayan kare muhalli daga dagwalo na matattun motocin dai, Abujar na kuma fatan karin kudin shiga daga kudin fiton motoci a cikin Najeriya da ke 'yan kasarta ke takama da arziki na Tokunbo. A bana kadai dai kasar ta dora wa hukumar hana fasa kwaurin kasar samo akalla Naira Triliyan Hudu domin tafi da harkokin kudin kasar da ke tangal-tangal.

To sai dai kuma in har mahukuntan na fatan kaiwa ga biya na bukata daga dukka na alamu suna shirin jefa 'yan kasar cikin karin rikici a cikin halin babu. Mafi yawa na kananan motocin dai na zaman kafar sufurin talakawa cikin kasar da ba ta da tsari na jiragen kasa.

Kuma aiwatar da tsarin dokar na iya kai wa ya zuwa kari na kudaden sufuri da kila ma daukacin harkoki na tattali na arziki.

Mohammed Mu'azu na sharhi cikin harkokin rayuwa da ci gaban al'umma a kasar da kuma ya ce ana bukatar kallon tsaf a cikin tsarin da nufin kauce wa kara jefa al'ummar kasa a cikin matsatsi.