1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan kwadago na yajin aiki a Kaduna

May 17, 2021

Kungiyar Kwadago a jihar Kaduna da ke Najeriya, ta sha alwashin fara yajin aiki saboda zaftare kudin ma'aikata da sallamar wasu dubbai da gwamnati ta yi.

https://p.dw.com/p/3tWNe
Nigeria Abuja | Protest für Mindestlohn vor Nationalversammlung
Kungiyar Kwadagon Najeriya ta saba dambarwa da gwamnati musamman kan albashiHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Masu dauke da cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA, sun bukaci ganin an yi sulhu da tattaunawa da gwamnati domin kauce wa wahalhalun da za su fada ciki. To sai dai a nata bangaren gwamnatin ta ce za ta barbaza jami'an tsaro domin magance ayyukan bata-gari da ka iya haifar da wata matsalar ta dabam.

Karin Bayani: NLC na adawa da sabon tsarin albashi 

Batun zaftare kudaden ma'aikata tare da sallamar wasu da dama dai, na daga cikin dalilan da suka sanya kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar fara wannan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar, domin sanar da gwamnatin jihar ta Kaduna cewa tura ta kai bango, wanda a saboda haka ne ya sanya kungiyar dakatar da duk wani akin gwamnati da na 'yan kasuwa har sai komai ya tsaya chak da nufin kwato wa maaikata 'yancinsu, kamar yadda shugaban kungiyar Kwamared Ayuba Magaji Suleman ya tabbatarwa manema labarai.