1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sakar wa kananan hukumomi ragamar kudi

Uwais Abubakar Idris AH
July 11, 2024

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin da ya bai wa daukacin kanana hukumomin Najeriya 774 cikakken yancinsu tare da haramta wa gwamnoni karbar kudaddensu.

https://p.dw.com/p/4iAyT
Hoto: Anacleto Delfim/DW

 Wannan hukunci da kotun kolin Najeriyar ta yanke ya bayyana cewa lamari ne da ya sabawa dokar tsarin mulkin Najeriyar gwamnaonin jihohi 36 na Najeriya su karbi kudadden kananan hukumomin don haka da yanzu kai tsaye za'a aikawa kanana hukumomin kudaddensu. Alkalin da ya jagoranci yanke hukunci a karar mai shari'a Emmanuel Agim  da ya jagoranci sauran lauyoyi guda shida ya bukaci a rinka bai wa jihohin kudaddensu  kai tsaye.

Alkalai sun yi amafani da hujoji 27 da duka suke a tsarin mulki ne wajen yanke wannan hukunci.

Die Last auf den Schultern der neuen Regierung - Nigeria vor der Wahl Flash-Galerie
Hoto: DW/Stefanie Duckstein

Dama dai gwamnatin Najeriya ce ta kai gwamnonin jihohi 36 na Najeriyar kara a gaban kotun kolin inda ta bukaci a ba su cikakken yanci kamar yadda yake a tsarin mulkin Najeriyar na 1999, domin duk da samun karin kudade ga kanana hukumomin bayan janye tallafin mai amma gwamnaonin ke murkushe kudadden inda talauci ke kara bayyana a matakan kanana hukumomi.  Alkalai sun yi amafani da hujoji 27 da duka suke a tsarin mulki ne wajen yanke wannan hukunci. Barrister Aliyu Anas Maigoro daya daga cikin lauyoyin da suka kare gwamnonin jihohi a wannan shari'a ya ce babbar  nasara ce.

Nigeria I Entführung am Federal College of Forestry Mechanization in Kaduna
Hoto: Stringer/REUTERS

Fiye da shekaru 20 kenana ana fafatawa a kan wannan batu kafin kai wa ga wannan mataki. A baya  dai an sha yunkuri ta hanyar mafani da majalisar dokokin wajen yi wa tsarin mullki gyaran fuska amma gwamnoni na kafar ungula a kan wannan, abin da ya sanya shugaban Najeriya bi ta kotun koli. Hin Muktar Dahiru Gora shi ne mataimakin shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriyar da suka dade suna gwagwarmaya a kan wannan batu.Ko wane tanadi kotu ta yi a kan nada shugabanin kananan hukumomi na riko da gwamnoni ke yi inda suke kin yin zabe lamarin da ka iya kawo cikas. Fiye da shekaru 20 kenana ana fafatawa a kan wannan batu kafin kai wa ga   wannan mataki.