1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cin bashi mai cike da rudani a Najeriya

July 5, 2024

A yayin da ake cigaba da kace nace bisa wata yarjejeniya ta nema na kudi na kasashen Turai, gwamnatin tarayyar najeriya tace bata da niyyar kare masu auren jinsi iri guda cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4hw3A
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da majalisar ministoci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da majalisar ministociHoto: Ubale Musa/DW

 

Kwadayi na wasu tsabar kudi har dalar Amurka miliyan dubu 150 ne dai ya dauki masu mulkin tarayyar najeriya zuwa rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da ake yiwa taken yarjejeniyar Samoa. Kasashe na Africa da Pacific da ma Caribbean dai na iya cin moriya na agaji daga tarayyar Turai a karkashi na yarjejeniyar in har sun amince su kare hakki na tsiraru dake a tsakaninsu. A bainar jama'a dai dama an gina yarjejeniyar ne bisa wasu jeri na muradu guda shida da ke jibantar kare hakki na tsiraru da mulki na gari, da batun tsaro dama zirga-zirga. Ko bayan alkintar yanayi da ingantaccen tattali na arziki.

Karin Bayani: Najeriya na ci gaba da haka rjiyar bashi

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da majalisar ministoci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da majalisar ministociHoto: Ubale Musa/DW

Makonni guda biyun da suka gabata ne dai Abujar ta hau sahu tare da rattaba  hannu bisa yarjejniyar da aka fara batunta tun a shekara ta 2018. Kuma a fadar Abdul Aziz Abdul Aziz da ke zaman mataimaki na kakaki na gwamnatin kasar, inda Najeriyar ta tabbatar da zare auren jinsin daga yarjejeniyar ta Samoa kafin kai wa zuwa ga rattaba hannu kanta.

A karkashin ta dai ratabba hannun na nufin amincewa da fuskantar kalubalen da masu auren jinsin ke fuskanta, da yin duk mai yiwuwa kan hanyar kai karshen. A wani abun da ake yiwa kallon babbar nasara a bangaren turawan da suka dauki lokaci suna matsa lambar neman dama ta wataya bisa hakkin na masu auren jinsi iri daya.