1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jan hankalin manoma domin tanadin abinci

November 22, 2023

Kungiyoyin manoman karkara da hukumomi na gargadin manoma da su kiyayyi sayar da amfani gonakinsu ga 'yan kasuwa saboda yada suke boye amfani gonar sai ya yi tsada su fitar su sayar.

https://p.dw.com/p/4ZJNb
Hoto: Ubale Musa/DW

A yayin da daukacin manoman arewacin  Najeriya  ke ci-gaba da girbe amfanin gonakinsu cikin wani yanayi na hauhawar farashin kayayyakin abinci ,da lallacewar hanyar mota wajan fito da abincin da suka noma tare da lallacewar tsaro. A wannan lokacin dai ,wata kungiyar da ke wayar da kan manoman Najeriya a kan  sabbin dabarun noma na zamani Agroceanic  Farmers association of Nigeeia ta fito fili karara ta gargadi manoman da ke saida abincin gonakinsu ga ‘yan kasuwa a irin wannan lokacin.

Fadikarwa zuwa ga manoma Najeriya don yin tanadi ga abinci da suka girbe

Kenia Landwirtschaft
Hoto: Billy Mutai/Sopa/Zuma/picture alliance

 Kungiyar ta shawarci manoman don yin takatsantsa ga masu zuwa gonakinsu suna saye amfanin domin boyewa,da zumar cin kazamar riba a nan gaba a cewar darektan ayyukan kungiyar Abdulramman Ali musa : ''Binciken da kungiyar ta gudanar ya gano yadda ake zuwa kauyuka dabam- dabam a jihohin arewa ana saye amafanin gonar,kuma ana biyan su kudade kadan,lamarin da ya sa  himmatu a kan fadikar da kananan manoman karkara irin hatsarin da ke tattare da wannan alamari”. Duk da cewa dai hukumomi da malaman addinai na ci gaba da gargadin masu saye amfanin gonar an boye, kungiyoyin da ke wayar kan manoma  na ci gaba a yi musu gargadi.