1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Rashin tsaro na mummunan tasiri kan noma a Filato

Abdullahi Maidawa Kurgwi MAB
July 21, 2023

Matsalar tsaro ta sanya daruruwan manoma na wasu yankunan jihar Filaton Najeriya dakatar da zuwa gonaki, duk kuwa da irin matakai da jami’an tsaro ke dauka don dakile hare-haren 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/4UEjs
Manoma na cikin mawuyacin hali sakamakon kalubalen tsaro a wasu sassan NajeriyaHoto: Luis Tato/AFP

Manoma da ke shiyyar tsakiyar Filato na ci gaba da zaman fargaba biyo bayan yawan hare-haren 'yan bindiga da ya  samo asali daga rikicin makiyaya da manoma, lamarin da ya yi sanadiyar rayuka da dimbin dukiyoyi a karamar hukumar Mangu. Ya zuwa yanzu  rundunar sojin Najeriya ta tura jami'anta inda suka kafa sansanoni a yankin, amma har zuwa manoma na tsorace a cewar Rabecca Simon 

Tun cikin watan Mayun 2023 ne aka soma fuskantar rikici a Mangu, yankin da ya yi fice wajen noman dankalin Turawa da masara. A  lokutan baya, 'yan kasuwa daga wajen jihar Filato kan yi jigilar anfanin gona  zuwa kasuwannin wasu jihohi Najeriya da ma kasashen ketare. Sai dai a yanzu, baya ga matsalar tsaro  manoman yankin na fama da karancin  kayyayakin aikin gona, a cewar Geman Alex, wani fittacen manomi. 

Nigeria Landwirtschaft Bauern
Ba a bar mata a baya a fannin noma ba a NajeriyaHoto: Ifiok Ettang/AFP

Karamar hukumar Bokkos ma ta sha fama da matsala ta rashin tsaro. Talatu Zakka da ta yi fice a noman dankalin Turawa ta ce tun ba yau ba suke fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga. Shi kuwa shugaban kungiyar manoman jihar Filato John Chindap Wuyep ya ce  hanya guda da za'a  rage radadin karanacin abinci a kakar bana shi ne kara daukan matakan tsaro  tare da  bunkasa noman rani .

Yanzu haka dai, hare-haren 'yan bindiga sun sanya daruruwan manoma  guje wa gonakinsu, yayin da wasu da rikicin ya raba wasu da dama daga muhallansu. Jama'a na fatan hukumomi za su kara azama wajen magance wannan matsala ta tsaro.