1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya amince da kasafin kudin 2023

January 3, 2023

A wa'adin mulkinsa na karshe da kuma kokarin cika alkawarin da ke tsakaninsa da al'ummar Tarayyar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2023.

https://p.dw.com/p/4LhMt
Najeriya |  Muhammadu Buhari | Shugaban Kasa | Kasafin Kudi
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Ubale Musa/DW

Duk da cewar dai ta dauki lokaci tana bugun kirjin iya kai wa ya zuwa cimma da dama, gwamnatin kasar 'yar sauyi dai na shirin kare wa'adinta ba tare da kamalla muhimman ayyukan da 'yan kasar ke fatan su gani ba. Kuma sabon kasafin kudin da ke zaman na farko mafi girma dai, na zaman damar karshe ga shugaban kasar da ke da babban burin wankin suna da kila ma kimarsa tsakanin miliyoyi na 'yan kasar da ke masa kallo na gazawa a cikin jan aikin na sauya rayuwa. Watanni kalilan ne dai ke gaban gwamnatin da ke kare wa'adi a watan Mayun da ke tafe, amma kuma ke kallon muhimmai na ayyuka na a ruwa. Ba a dai kammala babban titin da ya hade biranen Abuja babban birnin kasar da Kanon da ke zaman cibiyar cinikin arewaci ba, a yayin kuma da har yanzu akwai jan aiki a tsakanin matafiyan da ke fatan zuwa birnin Legas daga Badun.

Najeriya | Hanya | Kano | Abuja
Gaza kammala manyan ayyuka a Najeriya

Sanata Ahmad Lawal dai na zaman shugaban majalisar dattawa ta kasar, kuma ya ce ana bukatar kamalla manyan ayyukan da nufin daga darajar gwamnatin a idanun al'ummar kasa. An dai rattaba hannun ne a cikin yiwuwar fadawa wani sabon rikici, tsakanin bangaren zartarwar da ke fadin akwai aringizo tsakanin adadi na bangaren zartarwa da abun da masu doka ta kasar suka amince da shi. To sai dai kuma shugaban kasar ya ce babban burin zaben da ke gaban Najeriyar a halin yanzu ne, ya kai shi ga rattaba hannun a kasafin kudin da nufin kaucewa tsayawar lamuran zaben. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin bangarorin biyu dai, akwai dai tsoron yakin neman zaben da ke gudana yanzu na iya jawo koma baya ga kokarin aiwatarwa kasafin a watanni guda biyar da ke gaban masu tsintsiyar. To sai dai kuma bayan shekaru bakwai da doriya kan mulki, a tunanin masu mulkin na Abuja gwamnatin kasar ta yi nasarar cika alkawarin da ke tsakaninta da miliyoyin 'yan kasar a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na Abujar.