1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Kasafin kudi na karshe a mulkin Buhari

Uwais Abubakar Idris LMJ
December 28, 2022

'Yan majalisar dokokin Najeriya sun amince da kasafin kudin shekarar 2023 na sama da Naira tirliyan 21, duk da takadama da ta taso tsakaninta da bangaren zartaswa na kasar kan kasafin kudin shekarar 2022.

https://p.dw.com/p/4LVMz
Najeriya | Kasafin Kudi | Majalisar Dokoki
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kasafin kudin 2023Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

An dai kai ruwa rana tare da hatsaniya da ta kaure tsakanin 'yan majalisar dattawan da na tarayya, a game da bukatar da bangaren zartaswar ya aikawa majalisar na hallata masa kudin da ya kashe a shekaru bakawan da suka gabata na Naira tirliyan 22 ba tare da amincewar majalisar ba. Bayan jingine wannan batu 'yan majalisar sun amince da kasafin kudin na shekara ta 2023 da ke tafe.  Kasafin kudin na 2023 na da gibi sosai na kudin da za a aiwatar da shi, abin da wasu daga cikin 'yan majalisar suka nuna damuwa a kai. Abin daga hankali dai shi ne, yadda bangaren zartaswa ke kashe kudi ba tare da amincewar majalisar ba. Wannan ne dai kasafin kudi na karshe na wannan gwamnati, wadda ke kan karagar mulki tun daga shekara ta 2015.