1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MSF na kwashe jami'anta daga arewacin Najeriya

December 16, 2023

Doctors Without Borders, ta ce sakamakon rincabewar lamura a jihar Zamfara, ya tilasta mata janye wasu jami'anta da ke Zurmi inda ake yawan samun musayar wuta.

https://p.dw.com/p/4aEx1
Hoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Tsananin artabu a tsakanin kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da sojojin Najeriya a yankin arewa maso yammacin kasar, ya tilasta kungiyar likitoci masu ba da agaji na Doctors Without Borders kwashe wasu daga cikin jami'ansu daga yankin.

Wannan dai na nuni da irin kalubalen da ma'aikatan agaji ke fuskanta a arewa maso yammacin na Najeriya, inda 'yan bindigar daji ke kai hare-hare a kan fararen hula tare da gakuwa da su domin neman kudin fansa.

Kungiyar ta Doctors Without Borders, ta ce yadda yanayi ke kara rincabewa a jihar Zamfara, ya tilasta mata janye wasu jami'anta da ke Zurmi inda ake yawan samun musayar wuta a kusa da asibitin garin.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa ya damu da hare-haren da 'yan bindigar suka kai a garuruwan Zurmi da Maru da kuma Tsafe a baya-bayan nan.