1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da wa'adin mika mulki a Mali

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
January 3, 2022

Akasarin jam'iyyun siyasar kasar Mali sun yi watsi da wa'adin mika mulki na shekaru biyar da gwamnatin mulkin soja ta gabatar ga kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS KO CEDEAO.

https://p.dw.com/p/455zw
Putschistenführer Assimi Goita in Mali als Staatschef vereidigt
Shugaban gwamnatin juyin mulkin soja a Mali Assimi GoitaHoto: Habib Kouyate/XinHua/dpa/picture alliance

Cikin takardar da ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya tura wa shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da ke zaman shugaban ECOWAS ko CEDEAO na yanzu, daga ranar daya ga watan Janairun da muke ciki ne wannan wa'adi ya fara aiki. Yawan jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula da ke adawa da matakin sojojin Mali na ci gaba da kakkange madafun iko ya tasamma 10, ciki har da na tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta da jam'iyyar Yelema ta tsohon Firaminista Moussa Mara.

Karin Bayani: Matsalar tsaro da rikicin kabilanci a Mali

Dukkansu sun nunar da cewa wannan karin wa'adin shekaru biyar na mulki ya keta alkawarin da sojojin suka yi na mika mulki ga farar hula kafin karshen watan Fabarairu mai kamawa, ma'ana sun yi amfani da bakin talakawa wajen ci musu albasa. Wannan dalilin ne ya sa 'yan siyasar da farar hular Malin kin amincewa da gaban kanta da gwamnatin mulkin sojan ta yi wajen kara wa kanta wa'adi. Dama dai sun ki shiga kwarya-kwaryan zama da wakilan gundumomi suka yi, domin bayar da shawarwari kan sauye-sauye da ya kamata a gudanar a Mali. Wakilan gundumomi 725 da suka halarci taron, bayan zaman muhawara a kan batutuwa 13 da suka hada tsaro da tsarin gudanar da mulki sun tabo batutuwa da ke ci musu tuwo kwarya.
Badra Aliou Sacko shugaban riko na kungiyar FOSC ya ce karfin mulkin shugabanci, na daga cikin batutuwan da suka fi mayar da hankali a kai. Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, za su yi wani taro na musamman kan rikicin kasar Mali a ranar tara ga watan Janairun da muke ciki a birnin Accra, domin daukar matakan da suka wajaba. Idan za a iya tunawa dai, a ranar 12 ga watan Disambar bara, sun bukaci a gudanar da zabe a kasar Mali a watan Fabarairu tare da yin barazanar sanya karin takunkumi idan hukumomin mulkin sojin Mali suka ki mutunta wannan jadawalin na kafin 27 ga watan Fabrairun 2022. Sai dai gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta sanar da ECOWAS cewa ba za ta iya shirya zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a watan Fabarairun 2022 ba, sakamakon matsalar tsaro da wannan kasa mai fama da talauci ke fuskanta.

Ghana Accra| ECOWAS zur Lage in Mali | Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO Nana Akufo-AddoHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Karin Bayani: Matakan kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

Ana dai zargin sojojin na Mali da cin zarafin farar hula a yankunan da ke fama da tashin hankali, yayin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke ci gaba da kai hare-hare. A yanzu haka ma dai, kashi biyu bisa uku na fadin kasar ba ya hannun gwamnati. Sai dai malamin jami'a Ibrahima Ndiaye ya ce baya ga batun mika mulkin, akwai bukatar duba fannin ilimi da al'adu ma idan ana so Mali ta koma kan tafarki madaidaici. Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya kasance ja gaba, wajen kayyade shekaru biyar a matsayin wa'adin da sojojin za su yi a kan kujerar mulkin. Sai dai Sékou Niamé Bathily jami'in sadarwa na gamayyar jam'iyyu da kungioyyin farar hula, ya ce ya kamata a hanzarta shirya zabe domin mayar da Mali kan tafarkin dimukuradiyya.