1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Hukunci tsattsaura daga Faransa

Ramatu Garba Baba LMJ
June 4, 2021

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, kasarsa ta dakatar da aikin wanzar da zaman lafiyar da take yi a Mali, har sai lokacin da aka gudanar da zabe tare da mayar da kasar kan tafarkin mulkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3uRTA
Frankreich Mali - Militär Konflikte
Sojojin Faraansa na daga cikin sojojin kasashen ketare da ke kasar MaliHoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Wannan dai na zuwa ne, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi har sau biyu a cikin watanni tara a kasar ta Mali mai fama da aiyukan 'yan ta'adda. Matakin dai kamar fada ne da cikawa, domin kuwa tun a watan Agustan shekarar da ta gabata ta 2020, bayan da sojojin kasar ta Mali suka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta Faransan ta soma gargadi kan abin da ka iya biyo bayan juyin mulkin. Daya daga cikin barazanar da ta yi kuwa shi ne janye rundunarta da ta jima tana aikin taimakon Malin, don ganin kasar ta murkushe mayaka masu da'awar jihadi da suka hana zaman lafiya da ci gaban kasar.

Karin Bayani: Martanin ECOWAS ko CEDEAO kan Mali

Ana dai ganain Faransa da ke da kimanin sojoji 5000 da ta jibge a Malin, ba za ta iya cewa ya yi tasiri wajen shawo kan matsalar tsaron da Mali ke fuskanta ba, matsalar da ta kasance daya daga cikin daililan da suka janyo zanga-zanga na son ganin bayan mulkin Ibrahim Boubacar Keïta kafin Assimi Goïta ya jagoranci juyin mulki a kifar da gwamnatin shugaban da ake wa lakabi da IBK ba. Goïta da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar na riko ya ce, akwai abin da ya hango.

Mali Oberst Assimi Goita, neuer Übergangspräsident
Jagoran juyin mulki kana shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali, Assimi GoïtaHoto: AP Photo/picture alliance

Faransan dai ta ce umarnin dakatar da ayyukan sojojin kasarta, zai soma aiki nan take har sai an tabbatar da lokacin da gwamnatin rikon kwaryar za ta mika mulki ga sahihiyar gwamnati da za a samar bisa tafarkin mulkin dimukuradiyya, a zaben da aka tsara gudanar wa a watan Fabrairun 2022. Faransar ta kara da yin gargadi ga Mali, na gujewa yin wani juyin mulkin da ta ce, zai janyo ta yi mai gaba daya. Amma abu mafi muhimmanci ga kasar kamar yadda bangaren adawa ke fadi, shi ne fita daga cikin halin da Malin da ta kasance daya daga cikin kasashe matalauta a duniya ta yi.

Karin Bayani: Jamus ta tsawaita zaman sojojinta a Mali

Tun bayan hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta da sojoji suka yi a bara, aka soma samun tsamin dangantaka a tsakanin Faransa da Mali da ta yi wa mulkin mallaka. Duk wannan dai na zuwa ne, a yayin da kasar ta Mali  ke ci gaba da kasancewa a karkashin shugabancin Kanar Assimi Goïta wanda ya jagoranci juyin mulki har sau biyu a cikin watanni tara, ya kuma ayyana kansa a matsayin shugaban kasar a yanzu.