1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

September 3, 2020

Gwamnatin wucin gadi ta mulkin soja a Mali, ta fara tattaunawa da 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula, a wani mataki na cimma matsaya kan jadawalin kafa gwamnatin rikon kwarya.

https://p.dw.com/p/3hwjF
Mali Bamako Verhandlungen zwischen ECOWAS und Militärführern | Assimi Goita
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali ta soja Assimi Goita Hoto: Reuters/M. Kalapo

Yunkurin gwamnatin mulkin sojan Mali na tattaunawa da bangarori dabam-dabam na kasar. Kama daga bangaren siyasa na adawa da na masu mulki na da nasaba ne da yunkurin samun cikakkun shawarwari, game da yadda wa'adin mulkin gwamnatin wucin gadi karkashin jagorancin rundunar sojojin zai gudana. 

Karin Bayani: Rikicin siyasa ya saka Mali cikin tasku

Za a dai shafe tsawon kwanaki ana ci gaba da yin tattaunawar, wacce ke zaman irinta ta farko da ke shirin hada bangarorin kasar wuri guda. Masu sharhi kan al'amuran siyasar kasar na yi wa taron muhawarar kallon ba ya rasa nasaba da matsin lambar da sojojin ke fuskanta musamman ma daga waje, inda kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta mayar da kasar saniyar ware, tare da kakaba mata  takunkumai masu tsaurin gaske.  A wata hira da tashar DW, Jo Scheuer babban wakilin Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ko PNUD takunkuman, ka iya yin mumunar illa ga al'ummar kasar Malin.
Sai dai a daidai lokacin da ake shirin kaddamar da tattaunawa tsakanin bangarorin siyasa da na farar hula a kasar Malin, a hannu guda tuni al'umma suka fara jiran ganin yadda za a samu mafita kan halin kangin da suka fada, duk da yake a Bamako sun nuna gamsuwa da karbe mulkin da sojojin suka yi.

Mali I  Demonstration gegen Regionalblock ECOWAS in Bamako
Murnar juyin mulki a BamakoHoto: Reuters/J. Penney

Duk da wadannan  jerin takunkuman dai,  har yanzu Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tafiyar da aiyukanta a kasar Mali, to amma sai dai hukumar ta yi fargabar samun cikas wajen samun kudi zartar da wasu aiyukanta, inda yanzu haka ta ce wasu kananan ma'aikatanta sun dan fuskanci tangarda ta albashi, duba da rashin samun isasshen kudi daga bankuna.  

Sharhi: Matsalolin da ke tunkarar Mali

A yanzu wasu bayanai na nuni da cewar shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita mai shekaru 75 a duniya na fama da lalurar shanyewar barin jiki, bayan ya shafe tsawon lokaci ba tare da jin duriyarsa ko ganinsa ba musamman ga masu bibiyarsa ta shafukan sadarwa na Intanent, kasancewar a baya kusan kullum sai an ga sakonninsa bila adadin. A gabanin taronsu na tattaunawar dai, rundunar sojan ta Mali da ke rike da ragamar gwamnatin mulkin rikon kwarya a kasar, ta aiwatar da wasu muhimman sauye-sauye ciki har da nadin sabon shugaban hafsan hafsoshin rundunar.