1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Yanayin da 'yan jarida ke ciki

Mahaman Kanta LMJ
May 3, 2021

'Yan jarida na fuskantar matsaloli da dama ta fuskancin yada labarai. A daidai lokacin da ake bikin tunawa da 'yancin 'yan jarida, kafafen yada labarai sun gudanar da taro a Jamhuriyar NIjar.

https://p.dw.com/p/3surP
Afrika Pressefreiheit l Uganda - Protest für Pressefreiheit - Daily Monitor Zeitung
'Yan jarida na fuskantar tarin kalubale a AfirkaHoto: Getty Images/AFP/M. Sibiloni

A Jamhuriyar Nijar albarkacin zagayowar ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya, shugabannin kafofin yada labarai masu zaman kansu da ma mallakar gwamnati sun gudanar da taron yin bitar matsalolin da 'yan jarida suke cin karo da su da suka hadar da gagarumar barazanar da suke fuskanta daga hukumomin kasar.

Karin Bayani: Kokarin murkushe 'yan jarida a Najeriya

Rahotanni dai sun nunar da cewa 'yan jaridar na fuskantar matsaloli da suka hadar da na kame da musgunawa daga mahukuntan kasar, duk kuwa da cewa akwai tarin dokoki na dimukuradiyya da suka tanadi hakkoki da 'yanci na 'yan jaridun a kasar.

Karin Bayani: Aikin jarida cikin halin tasku a Najeriya

'Yan jaridar dai sun bayyana irin tarin kalubalen da suke fuskanta, musamman ma yayin zanga-zanga da sauran matsaloli da musamman kafafen yada labarai masu zaman kansu ke kokawa da su sakamakon kirkiro wasu sababbin dokoki da hukumomin suka yi da suka shafe wadanda aka tanada cikin dokoki na kasa da kasa.