1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kokarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

November 29, 2023

Masu shiga tsakani na kasa da kasa kan rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas na kara matsa kaimi don dorewar yarjejeniyar tsagaita buda wuta a zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4ZYlP
Kokarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a GazaHoto: Leo Correa/AP/dpa/picture alliance

Kwanaki shida bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a zirin Gaza, masu shiga tsakanin na kasa da kasa na kara matsa kaimi na ganin an dore da yarjejeniyar don kawo karshen rikicin da ya barke a ranar bakwai ga watan Oktoban da ya gabata.

Karin bayani:  Isra'ila da Hamas sun amince da karin wa'adin kwanaki biyu na tsawaita yarjejeniya sulhu

A cewar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ana sa ran tsawaita yarjejeniyar da sa'o'i 48 har i zuwa ranar Alhamis domin ba da damar sakin karin fursononin Isra'ila 20 da na Falasdinu 60 kamar yadda kasar Qatar babbar mai shiga tsakani a rikicin ta sanar.

Karin bayani: Za a sako karin mutanen a Gaza da Isra'ila 

A cewar kamfanin dillacin labaran Isra'ila an aike wa gwamnatin kasar jerin sunayen mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, sai dai har kawo yanzu ba a bayar da wani tabbaci a hukumance ba.

Ana dai sai ran nan ba da jimawa ba sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kai ziyara Isra'ila da Gabar Yamma da Kogin Jodan, yayin da ministan harkokin wajen Qatar Majed Al Ansari ya sanar da cewa suna iya kokarinsu don kawo karshen yakin baki daya.