1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta

November 27, 2023

Qatar ta ce Isra'ila da Hamas sun amince da karin wa'adin kwanaki biyu na tsawaita aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursinoni tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/4ZVLE
Hoto: Imad Creidi/REUTERS

Qatar ta ce Isra'ila da Hamas sun amince da karin wa'adin kwanaki biyu, hakan ya biyo bayan bukatar kasashen duniya na ci gaba da kiraye-kirayen tsawaita aiwatar da yarjejeniyar domin ci gaba da gudanar da ayyukan jinkai da kai kayan agajin gaggawa da kuma kubutar da karin wasu fursunonin yakin dake hannun bangarorin biyu.

Karin bayani:Gaza: Tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta 

Ko a baya-bayannan kalaman Firaiminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya nuna alamun bukatar karin wa'adin, inda a daya bangaren Hamas ta ce a shirye take wajen karin wa'adin na kwanaki hudu, idan har za a saki karin wasu fursunonin yakin na Falasdinu.

Karin bayani:Hamas ta sako mutane 17 a mataki na uku na musayar fursunoni da Isra'ila 

Hamas da wasu manyan kasashe ciki har da Amurka da Jamus suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, ta ce tuni ta aike da sunayen wadanda ta ke son a saki ga hukumomin Qatar da Masar da ke shiga tsakani, inda a gefe guda hukumomin Tel aviv suka mika sunayen wadanda suke so a kubutar.

Karin bayani: Akwai yiwuwar tsayar da aikin jinkai a Gaza

kawo yanzu dai an kubutar da 'yan Isra'ila dake tsare a hannun Hamas 58, yayinda Falasdinawa 177 suka shaki iskar 'yanci daga gidajen yarin Isra'ila.

271430 GMT Nov 23