1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Za a sako karin mutanen da ke tsare

Abdul-raheem Hassan
November 26, 2023

Rahotanni na cewa akalla Falasdinawa shida sun mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye a daren ranar Asabar, ranar ta biyu da fara aiwatar da yarjejeniyar sassauta fada da juna.

https://p.dw.com/p/4ZS3V
Yadda dangi suka hadu da 'yan uwansu da aka sakoHoto: Muammar Awad/Xinhua/picture alliance

Ofishin Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya karbi jerin karin sunayen mutanen da za a sako cikin wadan da mayakan Hamas ke rike da su, sai dai sakon da ofishin ya wallafa a shafin X bai bayyana ko mutane nawa za a sake ba.

Ana sa ran za a cigaba da musanyar mutanen da ke tsare a bangaren Isra'ila da Hama yayin da aka shiga rana ta uku cikin kwanaki hudu na yarjejeniyar tsagaita luguden wuta a zirin Gaza.

A matakin farko na yarjejeniyar, za a sake 'yan Isra'ila guda 50 da ke hannun kungiyar Hamas tun bayan fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2023, yayin da Isra'ila za ta sake Faladsinawa 150 da ke tsare a gidajen yarin kasar.

Jama'a sun gana da fursunonin Falasdinawa 39 dukkansu mata da yara a yankin yammacin Kogin Jordan da aka mamaye yayin da Isra'ilawa 13 da 4 'yan Thailand da aka kama suka isa Isra'ila.

Tuni dai motocin dakon kayan agaji suka fara shiga zirin Gaza da abinci da magunguna da sauran kayan masarufi, ana san cigaba da shigo da kayan agaji don kai doki ga dubban fararen hula da ke cikin wani hali a Gaza.