1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Sudan: Kokarin samar da zaman lafiya

August 15, 2024

Hankalin duniya na ci gaba da kasancewa a kan yadda za a iya nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan, kasar da ta fada yaki a cikin watan Afrilun bara.

https://p.dw.com/p/4jWZf
Sudan | Yaki | Tashin Hankali | Sulhu
Zaman tattaunawa domin kawo karshen yakin da aka jima ana gwabzawa a SudanHoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/picture alliance

Tattaunawar neman kawo karshen yakin na Sudan da ke cikin watannisa na 16 a birnin Geneva na kasar Switzerland, na cike da babban burin ganin hankali ya kwanta a kasar. Bayan samun samun daidaito a tarukan da aka yi a Bahrain da Saudiyya da ma kasar Masar a baya, Amurka da ke jagorantar taron kawo karshen yakin na Sudan ta nace har sai wani abun kwarai ya fito daga zaman da aka fara a wannan mako. Sai dai rashin ganin wakilan bangarorin da ke gaba da juna a zaman da aka bude shi a asirce, ya sake jefa shakku kan ko taron wannan karon na iya sauya wani abu. Cikin watan jiya ne dai hukumomin kasar Amurka suka fitar da sanarwar da ke alaka da taron na birnin Geneva, wanda aka tsara da hadin gwiwar Saudiyya.

Sudan | Yaki | Tashin Hankali | Sulhu
Yakin Sudan ya daidata kasar da ke yankin Arewacin AfirkaHoto: Mohamed Khidir/Xinhua/dpa/picture alliance

Sai dai tun daga lokacin 'yan jarida suka fara guna-gunin rashin samun gamsassun bayanai kan taron da ma wajen da za a yi shi, sannan ko wadanda ake sa ran su kasance za su halarta. Kasar Switzerland dai na da matukar kwarewa a kan abin da ya shafi shirya taruka makamantan wannan, saboda kasancewarta 'yar ba-ruwanmu da ma karfin tallafin da take bai wa batutuwa na jin-kai a duniya. Cikin watan na Yuli ne kuma wasu wakilan gwamnatin Abdel Fatta al-Burhan da na mayakan RSF suka ziyarci birnin Geneva, bayan karbar goyon gayyata daga manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kan rikicin na Sudan. Rashin ganin wakilan bangarorin biyu a taron ya sanya kakakin sakataren harkokin wajen Amurka Vedant Patel cewa, lallai ne taron ya ci gaba saboda halin da ake ciki.

Matsalar kasuwanci a yankunan Sudan da gwamnati da 'yan tawaye ke yaki

A bara lokacin taron da aka yi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a kan wannan batu na neman kawo karshen rikicin na Sudan, bangaren sojojin da ke mulki a Sudan sun ce ba za su halarci tattaunawar ba saboda a cewarta bangaren rundunar RSF da ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Mohamed Hamdan Dagalo bai tabbatar da abin da suka amince a rubuce ba. Abin da ya tabbata a yanzu dai tawagar wakilai daga bangaren rundunar RSF na halartar taron da ake yi a wani wajen da ba a bayyana ba, yayin da a share guda bangaren sojojin gwamnatin Sudan ke nuna rashin gamsuwa da tsarin taron da Amurka ta yi kuma ba su halarce shi ba. A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin na Sudan Tom Perriello ya ce taron na tafiya a halin da ake ciki, a kokarin da suke yi na ganin an kawo karshen zubar da jini da kuma cimma burin samun sakamako.