1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Mayakan RSF na kokarin kwace Darfur daga dakarun gwamnati

Mahmud Yaya Azare AH
July 30, 2024

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi kira ga MDD da tarayyar Afirka da su hada karfi da karfe wajen tura rundunar samar da zaman lafiya zuwa yankunan da aka yi wa fararen hula kofar rago.

https://p.dw.com/p/4iugS
Hoto: picture alliance / Xinhua News Agency

 Kamar yadda kakakin kungiyar ta Amnesty Slaver Pinches ya bayyana, daukar wannan matakin ne kadai zai iya kai wa ga ceton rayukan duban fararen hular da aka yi wa kofar rago musamman a garuruwan Al-Fasher da Shandy da ke yankin Darfur,wadanda mayakan RSF suke kokarin kwace shi daga hanun dakarun gwamnati.

Gargadin Amnesty International game da halin da farar hula ke ciki

Tschad Flüchtlinge aus Sudan Darfur
Hoto: ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

 ''Kisan kanmai uwa da wabi da ake yi wa fararen hula da ba su san hawa ko sauka ba,wadanda galibinsu yara kanana ne da mata, sakamakon musayen wutar da bangarori biyun ke yi cikin hauka ido rufe, abu ne da ba za a taba a zura ido ana ganin yana ci gaba da wanzuwa ba. Alhakin kare wadannan bayin Allah,a wadannan yankunan da ake zaman kara zube,ya rataya wuyan MDD da hukumomin kasa da kasa. Duk wani jinkirin daukar wannan matakin na nufin ,kara samuwar hasarar rayuka da ci gaban  ayyukan tarzoma.”

Dakarun RSF na kokarin kwace Darfur

Krieg im Sudan |  Armee schießt auf Kämpfer der Rapid Support Forces (RSF)
Hoto: @SUDANESEARMY1/UGC/AFP

 Tun a karshen mako ne dai, mayakan RSF,da suka yi wa birnin Alfasher kawanya, suka dinga yi masa lugudan wuta ba kakkautawa, a kokarinsu na kwace iko da birnin daya tilo da ya rage a hanun dakarun gwamnatin Sudan a yankin Darfur, lamarin da ya kai ga halaka kimanin fafaren hula 60 da jikkata wasu daruruwa gami da tserewar wasu dubbai zuwa daji da sansanonin 'yan gudun hijirar da ke jihohin Gadhareef da Al-Jazeerah,yadda galibin wadanda suka tseren ke dauke da raunuka suke kuma fama da yunwa, kamar yadda Lilly Andison,wani lIkitan hukamar lafiya ta duniya a sansanin  ya sanar.