1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

UNICEF: Yunwa na kashe yara a Sudan

Mahmud Yaya Azare LMJ
August 14, 2024

A daidai lokacin da yaki ke ci gaba da kazanta a sassa dabam-dabam na Sudan, Asusun Kula da Ilimin Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICE ya nuna taikaicinta ga yadda yunwa ta fara kashe kananan yara.

https://p.dw.com/p/4jTO5
Sudan | Yaki | Yara | Yunwa
Yakin Sudan ya saka yara da dama cikin taskun rayuwaHoto: Ebrahim Hamid/AFP

Shugabar Asusun Kula da Ilimin Kananan yara na Majalaisar Dinkin Duniya UNICEF Catherine M. Russell ce dai, ta nuna wannan takaici kan yadda karancin abinci a Sudan ta kai ga zama silar mutuwar daruruwan yara kanana a makon da ya gabata. Shugabar ta UNICEF ta kara da bayyana cewa, Sudan ita ce kasa mafi yawan yaran da suka rasa matsugunansu a duniya wasu miliyoyi kuma ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki da kuma rashin zuwa makaranta. Russell ta bayyana cewa akwai kimanin yara miliyan tara a Sudan da ba sa samun isasshen abinci yadda ya kamata, inda miliyan hudu daga cikinsu ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki.

Sudan | Yaki | Yara | Yunwa
Dubban mutane yakin na Sudan ya tarwatsa, baya ga asarar dimbin rayuka da dukiyoyiHoto: David Allignon/MAXPPP/dpa/picture alliance

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa, barnar da yunwa za ta yi a Sudan ka iya dara wacce yakin basasar da aka kwashe shekara guda ana yi muddin ba a gaggauta shigar da kayn agaji kasar ba. Wata mata da yunwa ta kashe 'yarta a yankin Kordofan a kudancin kasar ta Sudan, ta ce tana fata duniya ba za ta bar yunwar ta gama da sauran 'ya'yanta uku da suka rage wadanda suma a yanzu suke fama da yunwar ba. Majalisar Dinkin Duniyar dai, ta yi kira  ga bangarorin da ke gwabza yaki su gagauta bayar  da damar shigar da kayan agaji. Tun a farkon wannan watan na Agusta wasu kwararru a fannin kula da abinci suka yi hasashen cewa, zuwa watan Satumbar da ke tafe kaso 70 cikin 100 na al'ummar Sudan za su iya fuskantar matsananciyar yunwa.