1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamfanin NNPC zai sayar da man matatar Dangote a Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 14, 2024

Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta kasar Zacch Adedeji, ya ce ranar Lahadi za a fara hada-hadar rarraba man

https://p.dw.com/p/4kcbM
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kamfanin man fetur din kasar NNPCL ne zai dauki gabarar rarraba man da matatar man Dangote ke hakowa ga dillalan man kasar, da ya kai yawan ganga dubu dari shida da hamsin a ko wace rana, lamarin da ya kawo karshen takaddamar da aka jima ana fuskanta kan batun rarraba man.

Karin bayani:Majalisar Dokoki za ta sasanta Dangote da NNPCL

Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta kasar Zacch Adedeji, ya ce a gobe Lahadi za a fara hada-hadar cinikayyar rarraba man ga 'yan kasuwa a fadin kasar.

Karin bayani:An kaddamar da matatar man Dangote a Najeriya

Al'ummar Najeriya dai na fama da karancin man fetur a fadin kasar, a daidai lokacin da tsadarsa ke ci gaba da jefa jama'a cikin mawuyacin hali na kangin rayuwa.