1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya na fuskantar barazanar sabon nau'in corona

July 9, 2021

Masana kiwon lafiya a Najeriya, sun fara shawartar al'umma kan daukar matakan kariya domin yaki da sabon nau'in annobar corona mai suna DELTA da ya bulla a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/3wIKa
Coronavirus | Impfprogramm in Kenia
Hoto: Robert Bonet/NurPhoto/picture alliance

Bayan share tsawon watanni na ganin alamun sauki, Najeriya na fuskantar sabuwar barazanar ta'azzarar annobar COVID-19 tare da sabon nau'in cutar na Delta mai hadari. Tun daga watan Afrilun da ya shude, kasar ta fara ganin alamu na sararawa tare da yawan masu dauke da cutar corona na raguwa a kusan kullum. Amma bayan share tsawon makonni takwas, kasar ta shiga sabon zulumi tare da Cibiyar Kula da Cututtka ta kasar NCDC ayyana samun nau'in na Delta da ke zaman mai saurin yaduwa a tsakanin al'umma.

Karin Bayani   Matsalar kin zuwa gwajin corona

Wani matafiyi da ya shigo kasar daga kasar waje ne hukumar ta ce, ya kawo cutar a cikin Najeriyar a wannan makon.
Delta da tushenta ke kasar Indiya, a cewar kwararru na bazuwar da ta nunka ragowar nau'o'in annobar. Kwararrun sun ce, Delta na bukatar taka tsan-tsan a kasar da al'ummarta suka koma biki bayan dogon kullen annobar.

Impfung mit dem Biontech oder dem AstraZeneca Corona Impfstoff.
Akwai karancin allurar riga-kafin coronaHoto: Frank Hoermann/SvenSimon/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai kaso daya a cikin 100 na al'ummar kasar ne suka karbi zagayen farko na allurar riga-kafin AstraZeneca da kasar ke amfani da ita, a yayin kuma da rabin kashi ne kacal suka kai ga kammala allurar. Yanzu kuma babban hatsarin na zaman komawa bisa tsohuwar al'adar dauri da ta kalli uwar watsi da batun rufe hanci, da ma uwa uba tsaftar wankin hannu da sabulu. Kamfen na rashin imani da annobar, na karuwa a kafafen sada zumunta cikin kasar a yayin kuma da sabon nau'in ke ragargaza a kasashe na Asia da ma a nahiyar Afirka. Kasashe 16 da suka bayyana bullar nau'in Deltan a nahiyar ya zuwa yanzu, na ji har a tsakar kan da ya kai ga ninka yawan masu dauke da cutar a tsawon mako guda kacal. Jan aikin da ke gaban Najeriya na zaman iya sauya tunani na 'yan kasar da ke yi wa allurar riga-kafin annobar COVID-19 din  kallo irin na kurar kosau, ga kasar da har yanzu ke dogaro da Turawan yamma wajen babiya Allar allurar mai tasiri.