1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC na fuskantar babban kalubale

Salissou Boukari
October 11, 2018

Kalubalen jam'iyyar APC ga zabe mai zuwa

https://p.dw.com/p/36MVU
Karikatur: "Atiku emerging as PDP's presidential candidate"
Hoto: DW

A na iya cewa har ya zuwa wannan lokaci na bayan kammala tsayar da 'yan takara na shugabancin kasa a Najeriya da ma a matakai na jihohi, zuwa ga 'yan majalisu, kawuna na rarrabe a jam'iyyar APC, kuma a wasu jihohin irin su Zamfara ana ma hasashen yiwuwar tafiya zaben ba tare da 'yan takara a zaben gwamna da kuma 'yan majalisar dattawa da na wakilai ba. Sai dai kuma taron gwamnonin na APC da Shugaba Muhammadu Buhari, ya kasance wata babbar dama ta neman dinke baraka da kuma samun mafita.