1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da rikicin jam'iyya APC a Zamfara

Zulaiha Abubakar
October 11, 2018

Jam'iyar APC ta kasa ta rusa shugabancin jam'iyar a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeria cikin wata sanarwa da Sakataren jam'iyyar na kasa Mr Yekini Nabena ya rabawa manema labarai.

https://p.dw.com/p/364PE
Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Wakilinmu na jihar Katsina Yusuf Ibrahim Jargaba da a yanzu ke jihar ta Zamfara, ya ruwaito cewa sanarwar ta ce za ta tura wani kwamiti na musamman daga Abuja dan gudanar da zabukan fidda 'yan takarar a gobe Asabar, tare da gargadin jami'an gwamnatin jihar da sauran bangarorin da ke hamaiya da juna kan su guji cusa kansu a harkar zabukan.