1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Navalny ya ce rayuwarsa na cikin hadari

Binta Aliyu Zurmi MAB
March 25, 2021

Madugun adawa na kasar Rasha Alexei Navalny ya nuna fargaba dangane da lafiyarsa a sabili da azabtarwar da yake fuskanta ta hanyar hana shi barci a gidan yari.

https://p.dw.com/p/3rCC7
Alexei Nawalny | russischer Oppositionspolitiker
Hoto: Patricia De Melo Moreira/AFP/Getty Images

 Makusantan Navalny sun nuna damuwarsu a kan barazanar da azabtarwa a gidan yari ka iya yi ga rayuwarsa.

Alexei Navalny mai shekaru 44 da hauhuwa yayi suna wajen sukar muradin shugaba Vladimir Putin yanza fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu da rabi, ya ce wannan ba komai ba ne face bita da kulli.

A farkon shekarar nan ne mahukuntan na Rasha suka damke shi jim kadan bayan ya isa Moscow daga Jamus inda ya yi jinyar gubar da ya sha, wanda ake zargin mahukuntan na Rasha da sawa, zargin da suka sha musantawa a baya.

Tuni dai kasashen duniya ke ta kiran a sako shi amma abin ya ci tura.