1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Ta ziyarci Navalny a asibiti

Binta Aliyu Zurmi
September 28, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ziyarci madugun adawar kasar Rasha Alexei Navalny wanda ke kwance a wani asibiti a birnin Berlin inda ake duba lafiyarsa.

https://p.dw.com/p/3j7Sj
Berlin | Charité entlässt Kremlkritiker Nawalny
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Instagram/Navalny

Mai magana da yawun Merkel, Stefan Seibert shi ne ya tabbatar da wannan ziyara da shugabar gwamnatin ta kai wadda ya ce ta kashin kai ce, to amma sun yi wata ganawa ta daban wadda ba a kai ga sanin abin da ta kunsa ba, sai dai Alexei Navalny din ya wallafa a shafinsa na Twitter yana wa Merkel godiya da kulawar da aka bashi.

Wannn ziyara dai da alama ba za ta yi wa fadar Kremlin dadi ba, duk da ta musanta alakarta da binciken da kasashen Jamus da Faransa da Sweden suka yi  wanda ya nuna cewar da an sanya wa Navalny guba da ke sarke jijiyoyi.