1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

Isra'ila ta sake tsananta kai hare-hare a Gaza

October 28, 2023

Sojojin kasar Isra'ila na ci gaba da zafafa hare-hare a kan yankunan da ke gaza, inda suke fatattakar mayakan kungiyar Hamas da wasu kasashen duniya suka kira na ta'adda.

https://p.dw.com/p/4Y9jW
Guda daga cikin yankunan Gaza da ke fama da hare-hare
Guda daga cikin yankunan Gaza da ke fama da hare-hareHoto: AFP

Rundunar sojin Isra'ila, ta sanar da kara yawan hare-haren da take kaiwa a Zirin Gaza, inda ta bayyana kisan mayakan kungiyar da Hamas dama.

Ko a daren da ya gabata ma dai rahotanni sun tabbatar da kai wasu hare-haren akalla 150 a Zirin.

Kakakin rundunar ta Isra'ila, Daniel Hagari ya ce mayakansu za su ci gaba da luguden wuta a Zirin na Gaza da kewaye.

Kalaman na zuwa ne yayin da mayakan kungiyar Hamas daga nasu bangare ke cewa suna cikin cikakkiyar damara ta ci gaba da fafata yaki da Isra'ila.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guetrres ya bayyana mamakin ci gaba da kai munanan hare-hare da Isra'ila ke yi a Gaza, yana mai jaddada kiran da a tsagaita wuta domin samun damar kai agaji.

 Amurka da kasashen Tarayyar Turai duk sun dauki kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ta'adda.