1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta tsananta barin wuta a Zirin Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
October 27, 2023

Yakin da Isra'ila ke yi da kungiyar Hamas ya shiga makonni uku, kana rundunar sojin Isra'ila ta tsananta hare-haren a Zirin Gaza a kokarinta na kakkabe Hamas

https://p.dw.com/p/4Y8Et
Yadda hare-haren sojin Isra'ila suka tsananta a Zirin Gaza
Yadda hare-haren sojin Isra'ila suka tsananta a Zirin GazaHoto: AFP

Isra'ila ta ce ta kara tsananta barin wutar da take yi wa Zirin Gaza  a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas, a yayin da rahotanni a yankin ke cewa harin ya illata hanyoyin sadarwa sakamakon yadda sojin Isra'ila suka shafe tsawon sa'o'i suna luguden wuta kan yankin.

Karin Bayani:Isra'ila na son Antonio Guterres ya yi murabus

Ita ma kungiyar Hamas ta yi ikrarin cinna rokoki zuwa yankin Tel-Aviv da kuma yankin 'yan share wuri zauna na gabar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

Karin Bayani: Rokoki sun jikkata mutane a iyakar Masar da Isra'ila

Ma'aikatar harkokin tsaron Isra'ilar ta ce wannan farmakin na daga cikin masu muhimmanci da kasar ta kai kan mayakan Hamas tun bayan barkewar rikicin.