1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sojojin Isra'ila sun kutsa Zirin Gaza ta kasa

October 26, 2023

Gidan Rediyon sojojin Isra'ila ya ce sun samu gagarumar nasara a harin da suka kai Zirin Gaza ta kasa, a wani mataki na tunkarar tungar mayakan kungiyar Hamas da suka kai mata mummunan hari a kwanakin baya.

https://p.dw.com/p/4Y2dq
Isra'ila ta yi amfani da tankokin yaki a Zirin Gaza
Isra'ila ta yi amfani da tankokin yaki a Zirin GazaHoto: Jim Hollander/newscom/picture alliance

Isra'ila ta ce sojojinta sun kutsa arewacin Zirin Gaza ta kasa da tsakar daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis, a wani mataki na tunkarar  tungar mayakan kungiyar Hamas da suka kai mata mummunan hari a kwanakin baya. Gidan Rediyon sojojin Isra'ilar ne ya bayar da wannan sanarwa, yana mai cewar sojojinsu sun samu gagarumar nasara a wannan farmaki da suka kai ta kasa  ta hanyar amfani da manyan tankokin yaki.

Karin bayani: Netanyahu na shan suka a cikin gida

A daren Laraba zuwa Alhamis ne dai Firmainistan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa sojojin kasar sun kammala shirin kutsawa Gaza ta kasa. Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa dubu shida da dari biyar da arba'in da shida, yayin da Isra'ila kuma ta yi asarar mutane dubu daya da dari hudu, sai wasu 222 da 'yan kungiyar Hamas suka yi garkuwa da su.

Karin bayani: Za a ci gaba da kai kayan agaji a Gaza

Tuni ministan harkokin wajen Iran Hussein Amirabdollahian ya kai wata ziyarar ba zata kasar Amurka, don tattauna hanyoyin kawo karshensa, a taron da Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar nan gaba. Ma'aikatar harkokin kasar ta Iran ta ce Hussein Amirabdollahian ya sauka a birnin New York din Amurka domin nuna goyon bayan kasarsa kan batun kare bukatun Falasdinawa game wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.