1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kashe mutane 29 a wani sabon hari kan Gaza

August 18, 2024

Harin na Isra'ila ya zo ne a dai-dai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyara a yankin.

https://p.dw.com/p/4jbSS
Harin Isra'ila a Gaza
Harin Isra'ila a GazaHoto: Hadi Daoud/APA Images/ZUMA Press/picture alliance

Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce Isra'ila ta halaka mutane 29 a wani sabon harin da ta kai cikin daren Lahadi zuwa wayewar gari ciki har da wasu jarirai 'yan biyar.

Harin na zuwa ne a dai-dai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyara a yankin domin kokarin neman tsagaita wuta bayan shafe watanni ana tattaunawa.

Kasashen duniya na kira da a kawo karshen yakin Gaza

Masu shiga tsakani irinsu Amurka da Masar da kuma Qatar suka ce sun kusa cimma matsaya bayan shafe kwana biyu ana tattaunawa a birnin Doha na Qatar, ko da ya ke Amurka da Isra'ila na dan dari-darin nuna fatan samun nasara.

Rahotanni sun ce kungiyar Hamas ta nuna alamar rashin amincewa da wasu sabbin bukatun Isra'ila.

Isra'ila ta kai hari kan wata makaranta a Gaza

Kudurin yarjejeniyar da ake nema ya bukaci a samar da matakai uku, na farko shi ne Hamas ta saki dukkan mutane da ta kama a ranar bakwai ga watan Oktoban 2023, ranar da aka fara yaki tsakanin Isra'ila da Hamas.

Na biyu kuma shi ne Isra'ila ta janye duk sojojinta daga Gaza tare da sakin Falasdinawa da ta kama a matsayin fursunonin yaki.